Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rusa shugabannin ƙananan hukumomi

0
81
Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rusa shugabannin ƙananan hukumomi Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rusa shugabannin ƙananan hukumomi Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rusa shugabannin ƙananan

Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rusa shugabannin ƙananan hukumomi

A hukuncin da ta zartar a ranar Alhamis, kotun ƙolin tace, yin haka na iya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Kotun ƙoli ta haramtawa gwamnoni rushe majalisun ƙananan hukumomi da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya a faɗin Najeriya.

A hukuncin da ta zartar a ranar Alhamis, kotun ƙolin tace, yin haka na iya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

A ƙarar da Antoni Janar na tarayya ya shigar, gwamnatin tarayya ta buƙaci izinin kotun da zai hana gwamnoni yin gaban kansu wajen ruguje majalisun ƙananan hukumomin da aka zaɓa ta tsarin dimokuraɗiyya.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙoli ta umarci gwamnatin tarayya ta riƙa bai wa ƙananan hukumomi ƙuɗaɗensu kai-tsaye

Ƙarar ta Antoni Janar ɗin ya shigar na da hujjoji 27.

Waɗanda ake ƙara, gwamnonin jihohin Najeriya 36, sun ƙalubalanci antoni janar ɗin akan shigar da ƙarar.

Haka kuma, kotun ƙolin ta baiwa ƙananan hukumomin ƙasar 774 ‘yancin cin gashin kai akan gudanar da kuɗaɗensu.

A hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya zartar, Kotun Ƙolin ta caccaki gwamnonin game da tsawon lokacin da suka shafe suna tauyewa ƙananan hukumomin ‘yancin cin gashin kai.

Mai Shari’a Agim ya ƙara da cewar kamata ya yi ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 su riƙa sarrafa kuɗaɗensu da kansu.

Alƙalin ya kuma yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da gwamnonin da ake ƙara suka shigar tun da fari.

Kotun ƙolin ta ba da umarcin cewa da ga yanzu a riƙa aika kason kuɗaɗen ƙananan hukumomin da ke tahowa daga asusun tarayya garesu kai tsaye, a maimakon asusun gwamnatocin jihohi.

Leave a Reply