Kotun tarayya a Abuja ta ba da umarnin tsare mutanen da ake zargin ‘yan ta’adda ne
Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja ya sahalewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta tsare wasu mutane 10 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, da suka yi yunkurin kaddamar da kurkukun mayakan Boko Haram dana ISWAP a jihar Osun, tsawon kwanaki 60 har sai an kammala bincike.
Da yake hukunci a kan bukatar da lauyan mutanen ya gabatar, Mai Shari’a Nwite yace bukatar ta dace kuma ya amince da ita.
KU KUMA KARANTA:Hukumar DSS ta kama shugaban NLC, Ajaero
Daga bisani ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Maris domin fara sauraranta.
Ya kara da cewa an kama wadanda ake zargin ‘yan ta’addan ne a ranar 16 ga watan Disamban 2024, bayan da aka zargesu da hannu a ayyukan ta’addanci a karamar hukumar Ilesha ta jihar Osun.
Hukumar DSS ta binciken farko da aka gudanar ya nuna cewar wadanda ake tuhumar mambobin kungiyoyin boko haram da iswap ne kuma an kamasu ne sa’ilin da suke daukar horo akan yadda zasu kera tare da tada abubuwa masu fashewa.