Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari’ar Abba da Gawuna ranar Juma’a

0
124

Kotun Ƙolin Najeriya ta ce ranar Juma’ar nan za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Jihar Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta aika wa ɓangarorin biyu ranar Laraba da maraice.

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna sun tabbatar da cewa Kotun Ƙolin ta shaida musu cewa za ta yanke hukunci a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairun 2024.

Bayanai sun ce Kotun Ƙolin za ta bari
lauyoyi biyu daga kowane ɓangare su halarci zaman yanke hukuncin.

A watan Nuwamba da ya gabata ne gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya garzaya Kotun Kolin Najeriya bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da soke zaɓensa a matsayin gwamna.

Ya ɗauki matakin ne bayan Kotun Ɗaukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta Kano cewa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris na 2023.

KU KUMA KARANTA : Yau Kotun Ƙoli za ta saurari shari’ar Abba da Gawuna

A wancan hukuncin, Kotun ta cire ƙuri’a 165,663 daga ƙuri’un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa ƙuri’un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Sai dai jim kaɗan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja yana ƙalubalantar hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaɓen.

Amma a hukuncinta, Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba mamba ba ne na jam’iyyar NNPP a lokacin da aka gudanar da zaɓen 2023.

Wannan shari’a ta jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta fitar da wasu takardu da wasu ke ganin sun ci karo da hukuncin da ta yanke.

Ko da yake daga bisani Rajistara na Kotun ya ce hukuncinsu a bayyane yake.

Leave a Reply