Kotun Ƙolin Najeriya ta hana sakin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

Kotun Ƙolin Najeriya ta sauya hukuncin da wata ƙaramar kotu ta yanke na janye tuhume-tuhumen ta’addanci da ake yi wa jagoran ƙungiyar da ke neman ɓallewa daga ƙasar IPOB, Nnamdi Kanu, inda ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi.

A ranar Juma’a ne alkalkin Kotun Ƙolin Lawal Garba ya yanke hukuncin cewa a cigaba da yi wa Kanu shari’a kan tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci da ake yi masa a babbar kotun.

A shekarar 2015 aka fara shari’ar Kanu a Babbar Kotun Tarayya a Abuja, bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori tuhume-tuhumen a wani hukunci da ta yi a watan Oktoban 2022.

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar da hujja kan hukuncin da ta yanke na korar ƙarar a kan hujjar rashin bin ƙa’ida na mayar da Mista Kanu daga Kenya zuwa Nijeriya a watan Yunin 2021 domin ci gaba da shari’arsa.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kama wani babban kwamandan IPOB a jihar Inugu

Kanu, wanda ɗan Nijeriya mai takardar ɗan ƙasa ta Birtaniya da ke jagorantar ƙungiyar da ke fafatukar ɓallewa daga Najeriya IPOB, ya tsere daga Najeriya bayan tsallake beli a 2017. An kama shi a Kenya a 2021 tare da tuhumarsa da ta’addanci.

Kanu ya yi watsi da tuhume-tuhumen ta’adanci da ake masa da batun cewa yana sane yake watsa labaran ƙarya, waɗanda ke da alaƙa da saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta daga tsakanin shekarar 2018 zuwa bara.

Fafutukar da Kanu yake yi ta neman ɓalle yankin kudu maso gabashin Nijeriya na ƙabilar Ibo daga ƙasar ta zama sanadin da hukumomin ƙasar suka ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

Yunƙurin ɓallewar yankin kudu maso gabas a matsayin Jamhuriyar Biafra a shekarar 1967 – shekarar da aka haifi Kanu – ya haifar da yaƙin basasa na tsawon shekaru uku wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum miliyan ɗaya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *