Kotu ta yanke wa wani matashi hukunci ɗaurin rai da rai
Wata kotu a ƙasar China ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari bisa laifin kashe abokin karatunsa mai shekaru 13, lamarin da ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar kan yadda ake mu’amala da yara ƙanana.
Laifin, wanda ya faru a watan Afrilu, ya shafi wasu yara maza uku ‘yan ƙasa da shekaru 14 da cin zarafi tare da kashe abokin karatunsu, mai suna Wang, a wani gidan da aka yi watsi da su.
An bayyana cewa waɗanda suka aikata laifin sun kaiwa Wang hari da shebur (shovel) kafin su binne gawarsa, lamarin da ya ɗauki hankulan jama’a.
A ranar litinin wata kotu a lardin Hebei ta samu ɗaya daga cikin yaran mai suna Zhang da laifin kisan kai da gangan tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Wani yaro mai suna Li, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari, yayin da yaron na uku mai suna Ma aka tura shi aikin gyaran jiki bayan kotu ta ce bai cutar da wanda aka kashe ba.
Shari’ar tana daga cikin na farko da za a yi amfani da dokar ƙasar Sin da aka yi wa kwaskwarima, wadda ta rage shekarun aikata laifuka daga 14 zuwa 12 a shekarar 2021 saboda “laifuka na musamman” da suka shafi munanan laifuffuka da ke haifar da kisa.
Mai gabatar da ƙara ya ce, “Hanyoyin kisan sun yi muni musamman, kuma lamarin ya yi muni sosai,” in ji mai gabatar da ƙara, inda ya ƙara da cewa waɗanda ake tuhumar, duk da cewa ‘yan ƙasa da shekaru 14 a lokacin, sun ɗauki alhakin aikata laifuka a ƙarƙashin dokar ƙasar Sin.
KU KUMA KARANTA: An yanke wa wasu maza masu auren jinsi hukuncin ɗaurin shekara 100
Kisan kai a ƙasar Sin yana da hukuncin ɗauri ko kuma kisa, kuma wannan shari’ar ta sake haifar da tattaunawa game da daidaito tsakanin yin hukunci da kuma gyara ga masu laifi.