Kotu ta umurci CBN ta biya wani Bajamushe naira Miliyan 63 da ta tsare ba bisa ƙa’ida ba

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya biya wani Bajamushe, Martin Gegenheimer Naira miliyan 63.7 da dala 10,000 bisa kama shi da tsare shi da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya NIS ta yi ba bisa ƙa’ida ba.

A wani hukunci da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci babban bankin ƙasar CBN, da ya cire kuɗaɗen daga asusun gwamnatin tarayya da ke hannun ta, domin daidaita bashin da ya taso daga hukuncin 2021 da kotun alƙalai ta ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yankewa Najeriya.

Mai shari’a Ekwo ya yi watsi da bayanin CBN cewa, a halin yanzu asusun gwamnatin tarayya na cikin giɓi, wanda hakan ya sa ba za a iya biyan dukkan kuɗaɗen hukuncin ba.

KU KUMA KARANTA:An kashe fiye da mutum 60 a rikicin ƙabilancin ƙasar Papua, New Guinea

Bajamushen, wanda ya ce ya ziyarci Najeriya ne a wata ziyarar aiki, ya bayyana cewa, yayin da yake komawa Kenya a ranar 23 ga watan Fabrairun 2020, jami’an hukumar kula da shige da fice ta Najeriya sun tare shi a kofar shiga jirgin saman Kenya Airways bayan an kammala dukkan ka’idojin tashin jirgi.

Ya ce jami’an NIS sun kama shi, suka ƙwace fasfo ɗinsa tare da tsare shi a wani ɗakin da ke da cunkuso daga 23 ga Fabrairu, 2020 zuwa 4 ga Maris, 2020, duk da cewa akwai ƙa’idojin cutar COVID-19 da ya kamata a kula.

A ƙarshe dai ya ƙalubalanci kama shi da tsare shin da aka yi a gaban Kotun ECOWAS.

A cikin hukuncin ranar 4 ga Maris, 2021, wani kwamitin mutane uku na kotun , ƙarƙashin jagorancin shugaban kotun, Mai shari’a Edward Amoako Asante, ya bayyana kama Gegenheimer da tsare shi da aka yi a matsayin ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya shi N53,650,925 a matsayin diyya na musamman kan hasarar da ya samu da kuma kashe-kashen kuɗaɗen da ya yi a lokacin da hukumar NIS ke tsare da shi ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta kuma umurci gwamnatin Najeriya da ta sake biyansa diyyar Naira miliyan 10 a matsayin diyya ga duk wani laifi da rashin adalci da aka yi masa na tauye masa haƙƙinsa, sannan kuma ƙarin dala 10,000 da ya kashe yayin da yake neman beli.

Kotun ta ECOWAS dai ta umarci gwamnatin Najeriya da ta cire Bajamushen daga jerin sunayen da take sa ido, sannan ta gaggauta sakin fasfo dinsa na Jamus ba tare da wani sharaɗi ba, wanda jami’an gwamnatin Najeriya suka ƙwace ba bisa ƙa’ida ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *