Kotu ta umarci Hisbah ta ɗaura wa Ashiru Mai Wushirya aure da ‘Yar Guda nan da kwanaki 60

0
286
Kotu ta umarci Hisbah ta ɗaura wa Ashiru Mai Wushirya aure da 'Yar Guda nan da kwanaki 60
Mai Wushirya da 'Yar Guda

Kotu ta umarci Hisbah ta ɗaura wa Ashiru Mai Wushirya aure da ‘Yar Guda nan da kwanaki 60

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kotun Majistire mai lamba 7 da ke Kano karkashin Mai Shari’a Halima Wali ta umarci Hukumar Hisbah ta jagoranci ɗaura aure tsakanin Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda cikin wa’adin kwanaki 60.

Wakilin Hikima Radio ya ruwaito cewa kotun ta kuma umurci Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano da ya kasance mai lura da aiwatar da auren kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah ta bada sanarwar neman wasu fitattun ‘yan Tiktok shida a Kano

Mai Shari’a Halima Wali ta bayyana cewa idan aka kasa gudanar da auren cikin lokacin da aka kayyade, za a dawo da su gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da suka aikata.

Leave a Reply