Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Kotu ta tura wani gidan yari kan yi wa ’yar shekara 50 fyaɗe

Wani mutum ya tsinci kansa a gidan yari bayan an kai shi kotu bisa zargin yi wa wata ’yar shekara 50 fyade.

Babbar kotun jihar Edo ce ta tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari zaman sauraron hukunci.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa na yunkurin yi wa dattijuwar mai shekara 50 da haihuwa fyaɗe.

Lauya mai shigar da ƙara, Misis Ama Iyamu, ta shaida wa kotun cewa a ranar 27 ga Maris, 2023, a birnin Benin ne wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyaɗe.

KU KUMA KARANTA: Wani ya yi wa ƴar shekara 9 fyaɗe kuma ya kashe ta 

Barista Iyamu ta ce, wannan laifi ya saba wa sashe na 4 na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Edo, ta 2021, kuma laifin na da hukunci  a sashe na 5 (2) na wannan doka.

Bayan sauraron ƙarar ne Mai Shari’a Efe Ikponmwonba, ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yari

Ta kuma dage sauraron ƙarar zuwa ranar 8 ga watan Yuli  2024.


Comments

One response to “Kotu ta tura wani gidan yari kan yi wa ’yar shekara 50 fyaɗe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Kotu ta tura wani gidan yari kan yi wa ’yar shekara 50 fyaɗe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *