Wata Babbar Kotu a Kano ta sanya 17 ga watan Afrilun 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.
A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da kuma Lesage General Enterprises.
A ƙarar da Gwamnatin Kano ta shigar a kan waɗanda ake zargi su takwas, ta ce ta haɗa shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta amince Jacob Zuma ya tsaya takarar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu
An tsayar da ranar 17 ga Afrilun domin fara sauraron shari’ar wadda mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jiha mai lamba huɗu zai jagoranta.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi, ya tabbatar da cewa Ganduje, matarsa da wasu mutane shida a ranar da aka bayyana.
“Abin da shi [Ganduje] ya kasa fahimta shi ne, ba za ka iya guje wa ranar ƙin dillanci ba, tabbas za ta zo gare ka, kuma hakan ma zai zama izina ga dukkanmu da muke cikin gwamnati a yanzu.
“[Ganduje]Yana mai cewa ba za mu iya tuhumarsa amma ya manta cewa daga cikin laifukan da ya aikata akwai wadanda ke karkashin hurumin gwamnatin jiha.”