Kotu ta hana ‘yansanda kama Muhuyi Magaji

0
198
Kotu ta hana 'yansanda kama Muhuyi Magaji

Kotu ta hana ‘yansanda kama Muhuyi Magaji

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wata babbar kotu dake zaman ta a Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Sufeto Janar na ‘yansanda da hukumar ‘yansanda gayyata ko kamawa ko kuma musgunawa Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado.

Waɗanda su ka shigar da karar sun hada da antoni janar na jihar Kano, hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da Muhuyi Magaji Rimingado.

KU KUMA KARANTA:Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa

Haka kuma wadanda ake ƙarar sun hada da rundunar ‘yansandan Najeriya, Sufeto Janar na ‘yansanda, AIG shiyya ta daya, kwamishinan ‘yansanda na Kano, ASP Ahmed Bello da Bala Muhammad Inuwa.

Umarnin ya fito ne a ranar Litinin, a makon da ya gabata ne rahotanni su ka baiyana cewa ‘yansanda su ka kama Muhuyi tare da tsare shi tsawon awanni, inda daga bisani aka bada belin sa.

Rahotanni sun baiyana cewa an kama Muhuyi ne bisa zargin ƙwace wata kadara da ke da alaƙa da tsohon gwamnan Kano, kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Leave a Reply