Kotu ta hana CBN da RMAFC riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin Kano

0
26
Kotu ta hana CBN da RMAFC riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin Kano

Kotu ta hana CBN da RMAFC riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Babbar kotun Kano ta ba da umarni na dindindin ga gwamnatin tarayya kan riƙe wa ƙananan hukumomin Kano 44 kuɗaɗen su.

Mai shari’a Musa Ibrahim Karaye ne ya bada wannan umarni a yau Litinin, bayan karar da wasu wakilan kananan hukumomi suka shigar don kare ‘yancin su na karbar kuɗaɗe daga gwamnatin taraiya.

Waɗanda su ka shigar da ƙarar sun hada da shugaban kungiyar NULGE, Ibrahim Muhd da Ibrahim Uba Shehu da Ibrahim Shehu Abubakar da Usman Isa da Sarki Alhaji Kurawa da kuma Malam Usman Imam.

Waɗanda a ke ƙara sun hada da Akanta Janar na ƙasa, Babban Bankin Kasa, CBN da ‘Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission,(RMAFC)’ da kananan hukumomi 44 na Kano, bankin UBA da Access da kuma wasu bankuna shida.

Shari’ar ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da rabon kudaden kananan hukumomi, bisa zargin cewa an tafka magudi a zaben kananan hukumomin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta gudanar a watan Oktoba 2024.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci bisa zargin ɓatanci ga gwamnan Kano

Jam’iyyar APC ta shigar da karar hukumomi da dama na Gwamnatin Tarayya da na Jiha, ciki har da Babban Bankin kasa na (CBN), Kwamitin Raba Kudaden Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 na Kano.

Sai dai, kotu ta yanke hukunci cewa kananan hukumomi na da ‘yancin karɓar kudaden su, kuma ta haramta wa Gwamnatin Tarayya ko wata hukuma hana rabon wadannan kudi.

Da ya ke magana bayan hukuncin, lauyan da ya wakilci kananan hukumomi 44, Barrister Bashir Wuzirchi, ya bayyana cewa wannan nasara ce ga Jihar Kano.

“Mun shigar da wannan kara ne domin kare Kano daga masu son hana ci gaban jihar ta hanyar rike kudaden kananan hukumomi. Alhamdulillah, yau kotu ta yanke hukunci a kanmu, ta amince da duk bukatunmu, kuma ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta daina tsoma baki a cikin kudaden da doka ta tanadar wa kananan hukumomi,” in ji shi.

Leave a Reply