Kotu ta dakatar da CBN bai wa jihar Ribas kason kuɗinta na wata-wata

0
72
Kotu ta dakatar da CBN bai wa jihar Ribas kason kuɗinta na wata-wata

Kotu ta dakatar da CBN bai wa jihar Ribas kason kuɗinta na wata-wata

Wata Babbar Kotu a Abuja ta dakatar da Babban Bankin Najeriya CBN daga sakar wa gwamnatin jihar Ribas kason kuɗinta na wata-wata.

A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ce dukkan kuɗaɗen wata-wata da aka tura wa Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara tun daga watan Janairun wannan shekarar take dokar kundin tsarin mulki ne, kuma dole a dakatar da hakan.

Alkaliyar kotun ta ce gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 da Fubara ya yi a gaban ‘yan majalisar dokokin Ribas mai wakilai huɗu take dokar kundin tsarin mulkin ƙasar ne.

Mai Shari’a Abdulmalik ta ce abin da gwamnan ya yi babban cin mutunci ne ga kundin tsarin mulkin 1999.

Daga nan ne alkaliyar ta hana CBN da Akanta Janar na Tarayya da Bankin Zenith da Bankin Access Bank ci gaba da bai wa Fubara damar samun kuɗaɗe daga asusun tattara kuɗaɗen shiga da tarayya.

Tun da farko a watan Oktoba ne Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na ware naira biliyan 800 da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su biyar suka zartar wanda Edison Ehie ke jagoranta.

KU KUMA KARANTA: CBN zai ci gaba da ba wa gwamnati ƙayyadadden kashi 5 cikin 100 na bashi

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da ƙarar da Fubara ya shigar a kan rashin dacewar hakan.

Kotun ta ce Fubara ya janye ƙarar da ya shigar a ƙaramar kotu a kan lamarin don haka ba zai iya fara ɗaukaka kara ba a kan lamarin da bai ƙalubalanta ba a matakin shari’a.

A hukuncin da aka yanke, kotun ta ce ana sa ran Gwamna Fubara ya yi amfani da tsarin doka ba tsarin amfani da ƙarfi ba, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito.

Kotun ta ci gaba da cewa halin da ake ciki a Majalisar Dokokin Jihar Ribas tamkar mulkin kama-karya ne na Gwamna da kuma abin dariya da ya wuce gona da iri.

Mai Shari’a Omotosho ta soke kasafin kuɗin Ribas na 2024 da ‘yan majalisa masu goyon bayan Fubara suka amince da shi tare da ajiye batun gabatarwa da kuma zartar da kasafin kuɗin jihar Ribas na 2024.

A hukuncin da aka yanke Omotoso ta umarci gwamnan da ya sake gabatar da kasafin kuɗin ga majalisar dokokin da aka kafa bisa doka ƙarƙashin Martin Amaewhule.

Sannan ta umarci Fubara da ya saki duk wasu kuɗaɗen da aka tara a majalisar dokokin Ribas tare da hana gwamnan yin katsalandan a harkokin majalisar.

Leave a Reply