Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci bisa zargin ɓatanci ga gwamnan Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke kasuwa, ƙarƙashin Mai Shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ta aike da sammaci ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, da Faizu Alfindiki, ɗan APC bisa zargin yin batanci ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Wasu hadiman gwamnan, Amir Abdullahi da Ishaq Abdul ne su ka shigar da ƙarar, inda su ke zargin Abbas da Faizu da batanci ga gwamnan Yusuf ta hanyar WhatsApp da facebook.
A zaman kotun na yau, lauyan masu ƙara, Shazali Muhammad Ashiru, ya shaidawa cewa sun shigar da karar ne bisa kalaman da wadanda ake ƙarar ke yi.
KU KUMA KARANTA:Tinubu ya buƙaci Gwamnan Kano ya shiga tsakani kan rikicin Rimin Zakara
A cewar sa, “kalaman sun yi muni kuma za su iya haifar da tunzuri daga al’ummar jihar Kano masoya gwamna da ma halin mai girma Gwamna.
“Don haka sai mu ka ga cewa doka ta bada damar duk wanda ya ga ana wani abu da zai iya haifar da rashin kwanciyar hankali zai iya garzayawa zuwa kotu ya shigar da kara domin wanzar da zaman lafiya.
“Kalaman da Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sun yi muni ga muhibbar mai girma Gwamnan Kano kuma ko waye aka fadawa haka zai iya zuwa kotu ya nemi hakkin sa,” in ji lauyan.
Kotun ta kuma sanya 24 ga watan Fabrairu domin dawowa gaban kotun.