Kotu ta ɗaure ’yan canji 17 a gidan yari a Kano

0
42

Kotu ta yanke wa ’yan canji 17 a Kasuwar WAPA da ke Kano hukuncin daurin wata shida a gidan yarin.

Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa na Babbar Kotun Jihar Kano ya yanke musu hukunci ne bayan samun su da laifin aiki babu lasisi.

Sai dai kotun ta ba su zaɓin biyan tarar naira dubu 50 bayan sun amsa laifin da aka gurfanar da su a kai.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda sun tsare ’yan canji 17 a kasuwar WAPA

A makon jiya cewa ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kai samame a Kasuwar WAPA, inda suka kama wasu ’yan canji 17 kan zargin laifin aiki babu rajista.

A lokacin samamen jami’an tsaron sun kama kuɗaɗen ƙasashen waje da suka hada da Sefa 68,000 da kuma Rupee 30,000 a hannunsu.

Leave a Reply