No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar da ke yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon Kasa, EFCC, ta ce kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu kan samun shi da laifin yi wa rundunar sojin Amurka sojan-gona.

Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ne ya yanke masa hukunci bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa guda ɗaya da ake zarginsa da aikatawa.

Bayan yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu, Mai Shari’a Khobo ya ba shi zabin biyan tarar naira 150,000.

Sannan alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar Kassah wato Samusng Galaxy A02 wadda ya yi amfani da ita domin aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: An kama likitan bogi da ke ziyartar asibiti a Zamfara yana duba matsalar al’aurar mata

Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah ƙara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfara.

Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’a.

Zamba cikin aminci da yaudara na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta EFCC ke yaƙi da su a Najeriya.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta EFCC ta kama wani matashi wanda ake zargi da yi wa matar Sarkin Bichi zamba cikin aminci ta naira miliyan 20.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...