An yankewa Goni Muhammad da Saidu Sariki Hamani hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsu da laifin bayar da zinare na jabu, inda suka yi iƙirarin mallakin matar tsohon shugaban ƙasa Misis Patience Jonathan ne ga waɗanda ya saya.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kama su ne a ranar Alhamis, 28 ga Satumba, 2023.
An gurfanar da su a ranar 16 ga Mayu, 2022, a gaban mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno, Maiduguri, bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma karɓar kuɗi ta hanyar ƙarya har Naira 26, 492,000 (Miliyan Ashirin da Shida, ɗari huɗu da Naira dubu casa’in da biyu kacal).
KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure hakimi shekara biyar, bisa laifin safarar wiwi da miyagun ƙwayoyi a Sakkwato
Mai shari’a Kumaliya, a hukuncin da ta yanke, ta same su da laifi, ta kuma yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya zuwa bakwai a gidan yari kowannen su bisa laifin haɗa baki da kuma shekara bakwai bisa laifin aikata laifin ƙarya.
Za su fara zaman gidan yari ne daga ranar da aka fara gurfanar da su a gaban ƙuliya.