Kotu ta ɗaure mutane 4 da ake zargi da satar birkin jirgin sama guda 80
Kotun Majistare mai lamba 70 a jihar Kano ta tasa ƙeyar wasu mutane huɗu a gidan yari bisa samun su da laifin haɗa baki wajen yin sata.
Waɗanda ake zargin, Nuhu Auwalu, Yakubu Bala, Emmanuel Luka, da Safianu Abdullahi, sun yi awon gaba da birki na jirgin sama guda 80 daga kamfanin jiragen sama na Azman a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.
A cewar takardar tuhumar, jami’an tsaron kamfanin jiragen sama na Azman ne suka haɗa baki da waɗanda ake tuhuma domin aikata satar, wanda wani ma’aikacin kamfanin Otaru Bashir ne ya ruwaito shi a ranar 11 ga watan Disamba, 2024.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun gurfanar da Shamsiyya a kotu bisa zargin satar wayoyi a Kano
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin. A zaman kotun, an bayyana cewa an samu birki guda uku a hannun Yakubu Bala yayin bincike.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta tasa keyar waɗanda ake tuhumar zuwa gidan gyaran hali, sannan ta sanya ranar 11 ga watan Fabrairun 2025 mai zuwa domin ci gaba da shari’a.