Kotu ta ɗaure Bobrisky bayan ya amsa laifin wulaƙanta takardar naira

0
244

Alƙali Abimbola Awogboro na Babbar Kotun Tarayya dake Ikeja ya aika da Idris Olanrewaju da aka fi sani da Bobrisky zuwa gidan gyaran hali bayan da ya amsa laifin wulaƙanta takardar kuɗi ta naira.

Gabanin aikewa da shi zuwa gidan gyaran halin, Bobrisky ya cewa kotun ba shi da masaniya game da dokar da ta haramta cin zarafin takardar Naira.

Sai dai alƙalin kotun ya yanke masa hanzari da cewar, babu uzuri ga rashin sanin doka.

Sashe na 21 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta 2007 ya tanadi cewar, duk mutumin da aka samu da laifin jirkita yanayin ƙwandala ko takardar kuɗin Naira da CBN ya samar za’a iya zartar masa da hukuncin ɗaurin da bai gaza watanni 6 ba ko kuma tarar da ba ta gaza naira dubu 50 ba ko kuma a haɗa masa duka biyu.”

Lokacin da aka karanto masa laifinsa, Bobrisky ya yi iƙirarin aikata dukkanin tuhume-tuhume 4 dake da nasaba da wulaƙanta takardar naira.

KU KUMA KARANTA:Kotu a yi zaman farko don cire wa Bazoum rigar kariya

Sai dai gabanin a karanto tuhumar, lauyan Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin Najeriya ta’annati, Suleiman Suleiman, ya buƙaci kotun ta soke tuhuma ta 5 da ta 6 dake da nasaba da zarge-zargen halasta kuɗaɗen haram.

Daga bisani Mai Shari’a Abimbola Awogboro ya soke tuhuma ta 5 da ta 6.

Hakan ya share fagen gurfanar da Bobrisky akan tuhuma ta 1 zuwa ta 4 da suka taƙaita ga zarge-zargen cin zarafin takardar naira.

Da safiyar Juma’ar nan ne, jami’an Hukumar EFCC suka tisa ƙeyar Bobrisky zuwa kotun da misalin ƙarfe 9 da mintuna 12 na safiya cikin wata farar motar safa.

Idan ba a manta ba, a ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar EFCC ta cafke Bobrisky a bisa zarge-zargen cin zarafin takardar Naira da halasta kuɗaɗen haram.

Leave a Reply