Kotu a yi zaman farko don cire wa Bazoum rigar kariya

0
161

Wata kotun birnin Yamai ta yi zama a ranar juma’a 5 ga watan Afrilu ta 2024 da nufin nazari akan buƙatar cire wa hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum, rigar kariya a wani yunƙurin gurfanar da shi a gaban ƙuliya a bisa zargin cin amanar ƙasa.

A karshe kotun ta ayyana ranar 10 ga wata a matsayin ranar za ta bayyana hukuncin da za ta yanke.

Kotun ta Cour d’Etat mai mambobi kimanin 22, a zaman da ta yi a ƙarƙashin shugabancin Mai Shari’a Abdou Ɗangaladima a wannan juma’a 5 ga watan Afrilu ta mai da hankali ne kan buƙatar da ofishin Ministan Shari’a ya gabatar a madadin gwamnatin Nijar saboda ganin ta cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya a matsayin matakin share fagen shirye-shiryen gurfanar da shi gaban ƙuliya sanadiyar zargin cin amanar ƙasa.

Kusa a ƙungiyar fafutika ta ROTAB Mahamadou tchiroma Aissami na cewa bai ga matsala ba tattare da wannan mataki.

Lauyoyin hamɓararren shugaban ƙasar waɗanda Me Moussa Coulibaly ya wakilta a wannan zama, sun buƙaci kotun ta ɗage shari’ar zuwa wani lokacin na gaba ta yadda za su sami damar binciken takardun shari’ar, su kuma gana da mutumin da suke karewa.

KU KUMA KARANTA:An rusa majalisun ƙananan hukumomin Jamhuriyar Nijar

Sai dai haƙarsu ba ta cimma ruwa ba domin alƙalan kotun sun ayyana ranar 10 ga watan Afrilun dake tafe a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncin da za ta yanke.

Magoya bayan Shugaba Bazoum irinsu Sahanine Mahamadou da ke ganin rashin cancantar hanyoyin da aka bi a yunƙurin gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar ta Nijar na fatan ganin za a yi adalci a wannan harka.

Sakin Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa da ma muƙarraban gwamnatinsa na daga cikin sharuɗɗan da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da manyan ƙasashen duniya suka gindaya wa hukumomin mulkin sojan Nijar kafin su sake mayar da cikakkiyar hulɗa da wannan ƙasa yayinda mahukuntan ƙasar ke cewa abin na da kamar wuya saboda girman laifin da suke zarginsa da aikatawa.

A baya kotun CEDEAO ta umurci a sallame shi sai dai abin bai yi tasiri ba dalili kenan tun daga wancan lokaci kawo yau magoya bayan Shugaba Bazoum ke fassara matakin ci gaba da tsare shi a matsayin bita da ƙullin siyasa.

Leave a Reply