Kotu a Kano ta yankewa wasu ‘yan Tiktok 2 ɗaurin shekara 1 a gidan gyaran hali

0
17
Kotu a Kano ta yankewa wasu 'yan Tiktok 2 ɗaurin shekara 1 a gidan gyaran hali

Kotu a Kano ta yankewa wasu ‘yan Tiktok 2 ɗaurin shekara 1 a gidan gyaran hali

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wata kotun Majistiri a jihar Kano da ke zaune a gini mai lamba 47 a unguwar Norman’s land a ƙaramar hukumar Fagge ta aike da wasu ƴan TikTok su biyu gidan yari na tsawon shekara guda amma da zaɓin tara tun bayan karar da Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta shiga dasu kan zargin yada futsara a kafafen sada zumunta na zamani domin girbar abinda suka shuka.

Kotun ta samu ƴan TikTok ɗin biyu da laifin wallafa wasu bidiyoyi na rashin ɗa’a waɗanda suka ci karo da addini da kuma tarbiyyar malam Bahaushe tare da dokokin da suka kafa Hukumar ta tace fina-finai ta Jahar Kano.

KU KUMA KARANTA:Za mu iya canza matsayarmu kan rufe Tiktok a Amurka – Trump

Tun farko hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dau tsawon lokuta domin ganin yadda zata kama matasan ƴan TikTok su guda biyu wato Ahmad Isa da kuma Maryam Musa wacce akafi sani da Maryam madogara dukkanninsu yan unguwar Ladanai a yankin Hotoron jihar Kano.

A yayin gurfanar dasu a gaban kotun Lauyan gwamnatin jihar Barista Garzali Maigari Bichi ya tuhume mutanen biyu da haɗa baki wajen aikata manyan laifuka baya ga wallafa saƙon da ya ci karo da tarbiyyar addini da kuma dokokin jihar ta Kano, laifukan da dukkaninsu suka amsa aikatawa.

Hakan na kunshe cikin wata Sanarwa daga Abdullahi Sani Sulaiman Jami’in yada yada na Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano

Leave a Reply