Kotu a Kano ta wanke wani mutum daga zargin kisa bayan shekaru 23 ana shari’a
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Bayan fiye da shekaru ashirin cikin rashin tabbas, Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo a Kano ta wanke wani mutum mai suna Sabi’u Aliyu daga Unguwa Uku, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2002 bisa zargin kisan kai ba da gangan ba , saboda mutuwar wani mai babur.
An zargi Aliyu da haddasa mutuwar Ibrahim Wada Musa ba da gangan ba, a wani hatsarin mota, kuma aka gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar da abin ya faru.
Sai dai kotun ta ba shi beli bayan zaman farko na shari’ar.
Daga bisani kuma, aka dakatar da shari’ar sakamakon tarzoma da ta haddasa konewar ginin kotun.
KU KUMA KARANTA:Hukumar shari’a ta Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatan kotu
Shari’ar ta tsaya cak har na tsawon shekaru 23, kafin daga bisani a dawo da ita kwanan nan.
Bayan dawo da shari’ar, lauyan da ke kare Aliyu ya kalubalanci sake gurfanar da wanda ake zargi, yana mai cewa jinkirin da aka samu ya saba wa dokokin shari’a kuma ya tauye haƙƙin wanda yake karewa.
Lauyan ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar, yana mai jaddada cewa wa’adin da doka ta tanada don gurfanar da wanda ake zargi ya wuce.
A hukuncinsa, Khadi Aliyu Jibrin Danzaki ya amince da hujjojin lauyan, ya kuma wanke wanda ake kara, yana mai bayyana cewa karar ba ta da tushe a doka saboda kura-kuran da aka tafka wajen aiwatar da shari’ar da kuma jinkirin da aka samu na tsawon lokaci.









