Kotu a Kano ta tura ‘yan Tiktok 2 gidan gyaran hali

0
48
Kotu a Kano ta tura 'yan Tiktok 2 gidan gyaran hali

Kotu a Kano ta tura ‘yan Tiktok 2 gidan gyaran hali

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta kara aikewa da wasu yan TikTok biyu gaban kotu inda aka turasu gidan gyaran hali sati biyu kafin yanke hukunci.

Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano Alh. Abba El-Mustapha ya jaddada aniyarsa na kawo karshen aiyukan rashin da’a da ke faruwa a kafafen sada zumunta na zamani wato “Social Media” a Jihar Kano inda a Hukumar ta kara samun nasarar kama wasu matasa biyu yan TikTok da ake zargi da nuna rashin da’a tare da kaisu gaban kotu.

Kakakin hukumar tace fina-finan Malam Abdullahi Sani Sulaiman ya rawaito cewar tunda farko bayan mai gabatar da Kara Barr. Garzali Maigari Bichi ya karantowa wadanda ake zargin Isah Kabir da Fatima Adam laifinsu a nan take suka amsa, mai shari’a da ke kotun No-man’s-land Hajiya Halima Wali ta dage sauraran karar inda ta bada umarnin a ajiyesu a gidan ajiya da gyaran hali na Kano, har zuwa sati biyu domin sake samun ranar da za’a yanke hukunci.

KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta ba da horo ga mata 50 don su zama daraktoci a Kannywood

Idan ba’a mantaba a watanin da suka gabata Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta aike da irin wannan matasa gaban kotu domin ladaftar dasu inda kotun bayan samunsu da laifi ta yanke musu hukuncin daurin shekara daya ko zabin biyan tara na kudi nera dubu 100,000 ga kowanne su, tare da wanda zasu karbesu tare da sharadin irin haka bazai kara faruwa dasu ba.

Wannan wani yunkuri ne da Hukumar tace fina-finai ta ke yi tsawon lokaci domin kawo gyara tare da dakile irin rashin ta ido da wasu matasa ke nunawa a kafafen sada zumunta a Kano wanda yaci karo da al’ada tare da koyarwar addinin musulunci.

Leave a Reply