Kotu a Kano ta tura wani matashi gidan gyaran hali, bisa zargin lakaɗa wa matar babansa duka

0
263
Kotu a Kano ta tura wani matashi gidan gyaran hali, bisa zargin lakaɗa wa matar babansa duka

Kotu a Kano ta tura wani matashi gidan gyaran hali, bisa zargin lakaɗa wa matar babansa duka

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba ɗaya da ke zamanta a Kofar Kudu, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Shamsuddin Ado Abdullahi, Unguwar Gini, ta aike da wani matashi gidan ajiya da gyaran hali, bisa samunsa da lakada wa matar babansa duka har ya fasa mata idanu.

Tun da fari dai jami’an ƴan sanda ne suka gurfanar da Najib Aminu mazaunin Kwanar Dala da ke yanki karamar hukumar Dala a Kano bisa zarginsa da aikata laifin razanarwa da kuma haddasa rauni.

Lauyar gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Aliya Aminu Yar Gaya, ta karanto masa tuhumar, sai dai ya musanta tuhumar razanarwa, amma ya amince da tuhumar duka.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta ɗaure wani matashi shekara 1, bisa zargin fashi da makami

Mai shari’a ya kafa masa shaidun ikirari, sannan ya aike da shi gidan gyaran hali har zuwa ranar 15/9/2025 domin yanke hukunci da kuma kawo shaidu kan tuhumar da ya musanta.

Ana zarginsa da dukan matar babansa mai suna Maryam Ibrahim, har ya fasa mata idon hagu, saboda ta aiki kaninsa sayen awara.

Leave a Reply