Kotu a Kano, ta ba da umarnin a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar

0
34
Kotu a Kano, ta ba da umarnin a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar

Kotu a Kano, ta ba da umarnin a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar

Hukuncin na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya dake Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Simon Amobeda, ta dakatar da gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin.

Babbar kotun jihar Kano ta baiwa hukumar zaɓen jihar Kano mai zaman kanta (KANSIE) damar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin da aka shirya cewa za su gabatar a yau Asabar, inda ta soke duk wani yunƙurin jam’iyyun siyasa na dakatar da zaɓen.

Mai Shari’a Sanusi Ma’aji wanda ya jagoranci zaman kotun, ya zartar da cewar kundin tsarin mulki ya baiwa KANSIEC ikon gudanarwa da sanya idanu akan zabubbukan kananan hukumomi a ilahirin kananan hukumomin jihar Kano 44.

INEC ce dai ta shigar da kara tana kalubalantar jam’iyyar APC da wasu jam’iyyun siyasa 13.

A hukuncin da ya zartar, Mai Shari’a Ma’aji ya jaddada cewar za’a dauki duk wani yunkuri na kawo cikas a zaben a matsayin maras tushe da makama.

“KANSIEC, a bisa tanade-tanaden tsarin mulki, nada ikon gudanar da zabubbuka a jihar. Kuma duk wani yunkuri na kawo cikas a zaben ba shi da tushe a doka,” a cewarsa.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano za ta kafa rundunar tsaro a makarantu a Hedkwatar NSCDC

Haka kuma alkalin ya bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi yayin gudanar da zaben.

“Yana da matukar muhimmanci hukumomin tsaro su samar da tsaron da ya dace domin ba da kariya ga rayuka da dukiyoyi yayin gudanar da zaben a gobe, “ ya bada umarni.

Hukuncin na zuwa ne bayan da a Talatar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya dake Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Simon Amobeda, ta dakatar da gudanar da zabubbukan kananan hukumomi, inda ta kafa hujja da zargin cewa KANSIEC na aiki da kundin tsarin mulkin da ya sabawa doka.

Sai dai, hukuncin babbar kotun jihar Kano ya sahale a ci gaba da gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Leave a Reply