Kotu a Kano ta ɗaure wani matashi shekara 1, bisa zargin fashi da makami

0
245
Kotu a Kano ta ɗaure wani matashi shekara 1, bisa zargin fashi da makami

Kotu a Kano ta ɗaure wani matashi shekara 1, bisa zargin fashi da makami

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 20 karkashin Mai shari’a Musa Ahmad ta yanke wa wani matashi, Khalifa Usman Sheka, hukuncin ɗaurin shekara ɗaya bayan ta same shi da laifin aikata fashi da makami a unguwar Guringawa, Karamar Hukumar Kumbotso.

Kotun ta gano cewa tun a shekarar 2022 matashin ya kai hari shagon wata mata mai suna Hadiza Abdulrazak da ke Guringawa, inda ya yi mata fashi da makami tare da yankarta a hannu.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta yanke wa matashin da ake zargi da cinnawa budurwarsa wuta ɗaurin shekaru 15

Mai shari’a Musa Ahmad ya bayyana cewa kotun ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati, Barista Ibrahim Arif Garba, ya gabatar.

Sai dai lauya mai kare wanda ake tuhuma, Barista M.H. Ma’aruf, ya nemi sassauci ga mai laifin.

Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya, tana mai la’akari da cewa ya shafe tsawon shekaru uku a tsare tun bayan kama shi.

Leave a Reply