Kotu a Indiya na son a sauya wa wani zaki da matarsa suna saboda taƙaddamar addini

0
164

Wata kotu a Indiya ta buƙaci hukumomi da su nemo sabbin sunayen da za a sauya wa wasu zakuna mata da miji da ke da sunayen wata uwargijiyar mabiya addinin Hindu da kuma wani Sarki Musulmai, biyo bayan koke da wata kungiyar addini ta yi na son a raba musu wajen zama.

A wannan watan ne aka mayar da Sita da Akbar Gidan Namun Daji na Siliguri da ke Bengal, a wani shiri na musayar dabbobi a tsakanin jihohi maƙwabta.

Hakan ya harzuƙa ƙungiyar Vishwa Hindu Parishad (VHP), wata ƙungiyar addinin Hindu mai tsattsauran ra’ayi, wacce take nuna adawa da haɗin kan da ake son samarwa tsakanin addinai.

Ƙungiyar ta kai ƙarar ne a gaban kotu inda ta ce zaman tare da zakunan suke yi wani abu ne na “saɓo” da ya saɓa da aƙidar addinin Hindu.

KU KUMA KARANTA: Indiya ta ba wa Falasɗinawa kayan jinƙai

A ranar Alhamis ne Mai Shari’a Saugata Bhattacharyya na babbar Kotun Calcutta ya buƙaci lauyan gwamnati da ya sauya wa zakunan suna.

“Ya kamata a guji waɗannan sunaye kuma a daina kiran dabbobin da su don kauce wa ce-ce-ku-ce,” in ji shi, kamar yadda jaridar Hindustan Times ta rawaito.

Lauyan gwamnati, Joyjit Choudhury, ya shaida wa alkalin cewa, jihar ta riga ta fara tunanin sauya sunan dabbobin.

Sita na ɗaya daga cikin manyan jigogin almara na addinin Hindu Uwargijiya Ramayana kuma matar Ram, ɗaya daga cikin abubuwan bautar Hindu mafi girma.

Shi kuwa Akbar ya kasance Sarkin Daular Mughal a ƙarni na 16 wanda ya yaɗa mulkin Islama a yawancin yankunan Indiya – lokacin da ƙungiyoyin kishin addinin Hindu suka ce lokaci ne da ake zaluntar addininsu.

Ƙungiyar ta VHP ta kuma yi iƙirarin cewa tun asali an sanya wa Akbar sunan Ram kafin a kai zakaunan Siliguri.

Masu suka sun ce rashin yarda da addini ga tsirarun Musulmai miliyan 200 na Indiya ya ƙaru tun lokacin da gwamnatin Firaiminista Narendra Modi ta hau kan mulki a shekara ta 2014.

Ƙungiyar VHP da ke da alaƙa da jam’iyyar Bharatiya Janata ta Modi mai mulki, ta yi gangamin yaƙi da auren mabiya addinai daban-daban, tare da goyan bayan ƙoƙarin da wasu gwamnatocin jihohi ke yi na ganin an ƙara tsananta hakan.

Leave a Reply