Kotu a Abuja ta kori ƙarar da aka shigar don hana ICPC bincikar badaƙalar tallafin karatu na gwamnatin Kano

0
196
Kotu a Abuja ta kori ƙarar da aka shigar don hana ICPC bincikar badaƙalar tallafin karatu na gwamnatin Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Kotu a Abuja ta kori ƙarar da aka shigar don hana ICPC bincikar badaƙalar tallafin karatu na gwamnatin Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar Kotun Abuja ta kori ƙarar da wasu jami’an gwamnatin jihar Kano su ka shigar gaban ta da ta hana Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa da Dangogin su (ICPC) bincike kan zargin badaƙala a harkar tallafi karatu na jihar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, ICPC ta ce batun binciken ya zo ne sakamakon wani korafi da aka kai mata, ana zargin badaƙala a kuɗaɗen tallafin karatu na jihar Kano.

A sanarwar, ICPC ta ce bayan karɓar ƙorafin, ta gayyaci jami’ai a ma’aikatar ilimi mai zurfi da kuma ma’aikatar harkokin tallafin karatu na jihar Kano domin su bada bayanai da kuma takardu akan zargin.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya ba da tallafin karatu ga ɗaliban koyon Shari’a kimanin 221 a Yobe

Sai dai kuma a cewar ICPC, mai makon su amsa gayyatar da aka yi musu, sai jami’an, karkashin babban sakataren ma’aikatar ilimi mai zurfi, Hadi Bala, ya shigar da ƙara mai lamba 2857/2025 akan Antoni Janar na Ƙasa da ICPC, suna ƙalubalantar gayyatar ta su da cewa an haife musu hakkin su na ƴan kasa.

Sai dai da ya ke yanke hukunci akan ƙarar, alƙalin kotun, Mai Shari’a Obanor ya umarci a ƙara jami’an ma’aikatar tallafin karatu ta Kano a cikin ƙarar Sannan a cire Antoni Janar na Ƙasa daga ƙarar.

Alƙalin ya kuma ce takardar gayyatar da ICPC ta aike wa jami’an na gwamnatin Kano ta na nan a kan doka kuma ba a take hakkin su na ƴan kasa ba.

Daga karshe ICPC ta ce alƙalin ya kori ƙarar saboda rashin ingancin ta.

Leave a Reply