Kisan gilla biyar da suka tayar da hankali a Arewacin Najeriya baya bayan nan

Kisan da ake zargin wata matar aure ta yi wa wani matashi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya jawo ce-ce-ku-ce sakamakon yadda ake samun bayanai daban-daban da suke fitowa masu ɗaure kai.

Tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama Hafsat Surajo mai shekara 25 kan zargin kashe Nafiu Hafiz mai shekara 38.

‘Yan sandan sun bayyana cewa Hafsat ta amsa laifin da ake zarginta da shi inda ta ce ta caccaka masa wuƙa a sassan jikinsa daban-daban.

Sai dai a tattaunawar da ‘yan jarida suka yi da mahaifin marigayi Nafiu, ya ce yana fata hukumomi za su ɗauki matakin da ya dace da kuma yin adalci don kada lamarin ya kasance kamar yadda wasu irinsa suka kasance a baya.

A shekarun baya samu irin waɗannan lamura sau da dama a Najeriya musamman a Jihar Kano, sai dai har yanzu babu wani kwakkwaran hukunci da aka zartar game da kashe-kashen da aka yi.

Maryam Sanda

A watan Nuwamban 2017 aka zargi Maryam Sanda da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda ɗa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP Bello Halliru Mohammad.

Rahotanni a lokacin da lamarin ya faru sun ce Maryam ta samu saɓani da mijin nata ne wanda hakan ya kai ga ta caka masa wuka.

Bayan faruwar lamarin aka gurfanar da Maryam a gaban kotu inda alkali ya yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta.

Sai dai daga baya Maryam ta ɗaukaka ƙara inda ta zargin alkalin kotun da shari’a bisa son rai. Har zuwa yanzu babu wani ƙarin bayani game da ci gaban shari’ar Maryam.

Kisan Hanifa

Kisan Hanifa wadda yarinya ce mai shekara biyar a Kano ya yi matuƙar tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya kasance mai ban tausayi da takaici.

Bayan kisan Hanifa, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin garkuwa da Hanifa da laifin kisanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwa da ita.

Tun da farko malamin na su Hanifa ne ya haɗa kai da wasu domin sace ta inda daga baya ya kashe ta sannan ya binne ta a cikin wani buhu.

Sai dai tun bayan yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa, babu wani ƙarin bayani game da aiwatar da hukuncin na kisa a kansa.

Ummita da Ɗan China

A shekarar 2022 ne aka zargi wani ɗan ƙasar China mai suna Geng Quangron da kashe budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

Shi ma wannan lamarin ya tayar da ƙura wanda hakan ya sa aka shafe makonni ana tafka muhawara a shafukan sada zumunta.

A lokacin da lamarin ya faru, an zargi ɗan ƙasar Chinan da bin Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka wanda hakan ya yi ajalinta.

Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kuɗi sama da naira miliyan 60.

Sai dai har yanzu kotu ba ta yanke hukunci game da wannan lamari ba.

Mahaifiyar da ta kashe ‘ya’yanta biyu a Kano

A watan Oktoban 2020 ne kuma aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin wata uwa da kashe ƴaƴanta har biyu a Unguwar Sagagi.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku.

A shekarar 2020 ne wani lamari mai kama da almara wanda ya matukar jawo ce-ce-ku-ce ya faru a unguwar Sagagi a Kano bayan wata mata ta kashe ‘ya’yanta biyu.

Ana zargin matar da kashe ‘ya’yanta biyu wadanda suka hada da Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da Zahra’u Ibrahim mai shekara uku bayan mijin ya yi barazanar yi mata kishiya.

Sai dai a bayanin da iyayen matar suka yi wa ‘yan sanda, sun ce ‘yarsu na da taɓin hankali tsawon shekaru


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *