Kimanin mutane dubu ɗari ne suka gudanar da sallar Edi a masallacin al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudu a safiyar Laraban nan.
An dai gudanar da sallar ce a cikin tsauraran matakan tsaro, ganin yadda sojojin Isra’ila ke duba katin shaidar masallata kafin basu damar shiga cikin masallacin.
Haka nan Falasɗinawa da dama ne suka gudanar da sallar Idi a rusasshen masallacin al-Farouk da ke Rafah a safiyar yau.
A sakonsa na taya al’ummar Musulmi barka da Sallah, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterresya nuna rashin din dadinsa gama da yadda rikice-rikece suka shafi mabiya addinin Musulci a Gaza da sauran sassan duniya.
A cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Guterres ya ce yana cike da takaicin yadda al’ummar Musulmi a Gaza da Sudan da sauran wasu kasashe ke cikin kunci saboda yaki, da hakan zai sa wasu da dama ba za su samu damar gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala ba.