Kimanin mutane 30 ne suka mutu a zaftarewar ƙasa a Kamaru

0
228

Zaftarewar laka a ƙasar Kamaru, ta janyo rugujewar gidaje 25.
Adadin mutanen da suka mutu sanadin zaftawar ƙasa ranar Lahadi a Yaounde babban birnin ƙasar Kamaru ya ƙaru zuwa mutum 30, yayin da ƙarin 17 suka ji raunuka.

Ministan cikin gidan Kamaru wanda ya je wurin da abin ya faru ne don ganin irin ɓarnar da aka yi ya sanar da haka.

Gidaje da dama a Mbankolo, wata unguwar masu ƙaramin ƙarfi, sun ruguje sun zama baraguzai, bayan wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. Haka kuma akwai fargabar cewa ƙarin mutane ne gine-gine suka rufta da su kuma har yanzu ba a kai ga gano su ba.

KU KUMA KARANTA: Mutane 30 sun mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a Abuja

“Mun sanya ayarin jami’ai da zai ci gaba da aiki tsawon rana don gano mutane,” kamar yadda ministar gidaje da raya birane, Celestine Ketcha Courtès ta faɗa wa BBC.

Daga cikin waɗanda aka kuɓutar, har da jariri ɗan wata uku.

Hukumomi sun buƙaci mazauna unguwar wadda ake ɗauka a matsayin yanki mai hatsari, su fice daga cikinta saboda fargabar sake aukuwar zaftarewar ƙasar.

Mazauna unguwar sun faɗa wa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da ruwan sama ya tumbatsa a wani kogin yanki. Mutanen da suka yi asarar komai nasu, sun ce ba su da wani wuri da za su iya zuwa.

Wani gidan rediyon yankin ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 40. Ambaliyar ruwa na ci gaba da kawo cikas ga ayyukan ceto, abin da ya tilasta wa mutane yin amfani da hannuwansu wajen zaƙulo gawawwaki daga cikin laka.

Iftila’in ya zo ne kusan shekara ɗaya bayan aƙalla mutum 14 sun mutu a wata zaftarewar lakar da ta faru a birnin.

Unguwar talakawa ta Mbankolo ce iftila’in ya fi muni a lamarin na baya-bayan nan, inda gidajen da aka gina a gangare, suka ruguje, ambaliya ta jijjige bishiyoyin ayaba.

An ga gawawwakin ƙananan yara “kwakkwance a kan taɓo, wani mazaunin unguwar ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta ‘Cameroon Voice’.

Leave a Reply