Connect with us

Ƙasashen Waje

Kenya ta soma sauraron ƙararraki kan zargin cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi

Published

on

Kenya ta soma sauraron ƙararraki kan zargin cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi

Kenya ta soma sauraron ƙararraki kan zargin cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi

Kenya za ta soma zaman sauraren ƙararrakin jama’a a ranar Talata kan zargin take hakkin ɗan’adam da kuma cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi a kasar wadda ta taba yi wa mulkin mallaka.

Sashen horar da sojojin Birtaniya a Kenya (BATUK) wuri ne na tafiyar da ayyukan da suka shafi tattalin arzikin mutane da dama a tsakiyar garin Nanyuki, inda aka kafa sansanin soji na dindindin, amma kuma ana zargin sojojin da ke wurin da aikata laifuka ciki har da kisan kai.

Ɗaya daga cikin manyan laifuka da suka fi ɗaukar hankali a shekarar 2012, shi ne na tsintar gawar wata mata ‘yar ƙasar Kenya a cikin wata rijiya a Nanyuki, inda ganinta da rai na ƙarshe da aka yi tare da wani Sojan Birtaniya ne.

Iyalan Agnes Wanjiru sun shigar da ƙara a Kenya kan mutuwar matashiyar mai shekaru 21, amma babu wani ci gaba da suka samu kan shari’ar, inda aka yi ta ɗage sauraron ƙarar.

Yanzu dai ana sa ran sake sauraron ƙarar a ranar 10 ga watan Yuli kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasar suka rawaito.

A makon jiya ne majalisar dokokin Kenya ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman sauraron ƙararrakin jama’a har guda hudu ciki har da na Nanyuki kan cin zarafin da ake zargin sojojin Birtaniya da aikatawa a ƙasar.

Za a yi zaman sauraron ƙararrakin ne tsakanin ranakun Talata da Alhamis na wannan makon inda za gudanar da ”bincike kan zarge-zargen take hakkin bil’adama da suka haɗa cin zarafi da azabtarwa da tsare mutane ba bisa ka’ida ba da kuma kashe- kashe,” a cewar wata sanarwar da majalisar ta fitar.

KU KUMA KARANTA: Ana fargabar zaftarewar ƙasa ta rutsa da mutane da dama a Kenya

Kazalika zaman zai yi duba kan “zargin take hakkokin ɗa’ar aiki da suka haɗa da cin hanci da rashawa da aikata zamba da kuma nuna wariya da cin zarafi da sauran munanan dabi’u.”

Birnin Landan da Nairobi suna takun-saƙa kan batun hukunta sojojin Birtaniya da suka take dokokin Kenya, inda a baya gwamnatin Birtaniya ta ce ba ta amince da hurumin kotun Kenya na bincike kan kisan Wanjiru ba.

Da yake amsa tambayoyi kan sauraron karar na wannan makon, mai magana da yawun hukumar Biritaniya ya shaida wa kamfanin dillacin labarai AFP cewa: “Hukumar Birtaniya a Nairobi da BATUK suna da niyyar ba da hadin kai ga binciken.

“Haɗin gwiwar ayyukan tsaro na Birtaniya da Kenya na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan dangantakarmu kuma horon da muke samarwa ta haɗin gwiwa da ayyukan da muke yi tare suna taimakawa wajen samar da tsaro ga al’ummar Kenya da Birtaniya,” in ji shi.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne tawagar Birtaniya ta ce babban kwamishinanta Neil Wigan ya gana da iyalan Wanjiru, waɗanda suka dade suna neman a yi musu adalci kan kashe ta da aka yi.

“Taron ya ba da dama ga Babban Kwamishinan ya saurari ‘yan’uwan marigayiyar tare da yi musu ta’aziyya. Kazalika ya samu damar jaddada matsayar Birtaniya na ci gaba da bayar da cikakken haɗin kanta ga binciken da Kenya ke yi kan (mutuwar Misis Wanjiru),” in ji sanarwar.

A watan Oktoban 2021 ne, Jaridar ‘The Sunday Times’ ta Biritaniya ta ruwaito cewa wani soja ya shaida wa abokansa cewa sun kashe Wanjiru kuma ya nuna musu gawarta.

Rahoton ya yi zargin kan cewa an sanar da manyan jami’an soji game da kisan, amma ba a dauki wani mataki akai ba.

An ƙaddamar da bincike kan batun ne a shekarar 2019 amma ba a bayyana sakamakon ba ga al’ummar.

‘Yan sandan Kenya sun sanar da cewa za a sake buɗe binciken bayan rahoton da Jaridar Sunday Times ta fitar.

Iyalan Wanjiru sun shigar da karar sojojin Birtaniya a Kenya da kuma ‘yan sanda da jami’an shari’a da na siyasa na Kenya kan batun mutuwarta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Published

on

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Daga Ibraheem El-Tafseer

Me magana da yawun Shelkwatar zaɓe ta Iran Dakta Muhsin Elsami, ya sanar da cewa, an kammala lissafi ƙuri’a Miliyan 25 na zaɓen shugaban ƙasar Iran wanda aka fara ranar juma’a.

‘Yan takara 6 ne suka tsallake matakin ƙarshe yayin da 2 suka fice saboda ra’ayin kai, ana zaɓe saura kwana 2.

Dakta Mas’ud Pezeshkian shi ne kan gaba da ƙuri’a Miliyan 10.415.991

Dakta Sa’ed Jalili ya samu ƙuri’u Miliyan 9.473298

Se kuma Dakta Qalibaf ya samu ƙuri’a Miliyan 3.383.340

Sai Ayatullah Musfata ya samu ƙuri’a 206.397.

Yanzu haka an fitar da Dakta Baqir Qalibaf da Ayatullah Musfata da suke da ƙarancin ƙuri’a, ya rage saura Dakta Jalili da Dakta Mas’ud Pezeshkian da ken gaba.

KU KUMA KARANTA: Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Jami’i Muhsin Elsami ya sanar da cewa za’a shiga matakin zaɓe na 2 ranar Juma’a mai zuwa inda za a kara tsakanin Dakta Jalili da Dakta Mas’ud.

Cikin su duk wanda ya samu kaso 50 ya zama shugaban ƙasar Iran, wanda zai maye gurbin Shahid Ebrahim Ra’isi wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin Helikofta, a watan da ya gabata.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra’ila kan Shugaba Erdogan

Published

on

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra'ila kan Shugaba Erdogan

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra’ila kan Shugaba Erdogan

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi Allah wadai da wani saƙo da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Israel Katz ya wallafa a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan kan shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na Isra’ila na ɓoye laifukanta.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a ranar Talata ta ce “Muna daukar wannan matsayi na rashin mutuntawa da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila ke yi wa mai girma shugaban kasarmu a matsayin wani lamari da za a ji shi ne kawai daga bakin ƙasar da ake zarginta da kisan kiyashi.”

Yayin da take suka da kakkausar murya a shafukan sada zumunta, ma’aikatar ta ce: “Irin wannan ƙazafi da ƙarya wani ɓangare ne na ƙoƙarin Isra’ila na ɓoye laifukan da ta aikata.”

Turkiyya ta ƙara da cewa, za ta ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da adalci.

KU KUMA KARANTA: Ana lalata mutuncin bil’adama a Gaza – Ministan Turkiyya

Isra’ila, wadda ta yi fatali da ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman tsagaita wuta cikin gaggawa, ta fuskanci tofin Allah-tsine a tsakanin kasashen duniya a ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Fiye da Falasɗinawa 37,700 aka kashe tun daga lokacin a Gaza, yawancinsu mata da yara, kuma kusan wasu 86,400 sun jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Sama da watanni takwas da yakin Isra’ila a Gaza, inda yankuna da dama suka zama kufai a cikin yankin da aka yi wa ƙawanya da hana shigar da abinci da ruwan sha da magunguna.

Ana tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Duniya, wanda hukuncin na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasɗinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like