Kenya ta janye shirin ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati

0
56
Kenya ta janye shirin ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnati

Kenya ta janye shirin ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati

Kenya ta dakatar da shirinta na kara albashin ‘yan siyasa masu riƙe da madafun iko daga 1 ga watan Yuli.

A ranar Larabar nan ne Hukumar Kula da Albashi da Jindadin Ma’aikata ta bayyana cewa ta “dakatar da shirin ƙara albashin dukkan ‘yan siyasa masu riƙe da madafun iko, kuma za ta yi duba ga shawara kan albashin dukkan ‘yan siyasa don tabbatar ɗorewar kashe kuɗaɗe.”

Shugabar Hukumar Lyn Mengich ta ce an yanke hukuncin dakatar da shirin ƙarin albashin ne bayan tattaunawa da neman shawarwarin jama’a.

Hukumar ta SRC ta fitar da wata sanarwa a hukumance a jaridar Gwamnatin Kenya a watan Agustan 2023 inda ta bayyana shirinta na ƙara albashin ‘yan siyasa masu riƙe da madafun iko daga 1 ga Yulin 2024.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Ruto na Kenya ‘ba zai’ sa hannu a kan sabuwar dokar ƙarin haraji ba

Shugaban Ƙasar Kenya William Ruto ya umarci Ma’aikatar Kuɗi ta ƙasa da ta dakatar da shirin ƙarin albashin.

Shugaba Ruto ya ce wannan mataki zai taimaka wa Kenya ‘Ta rayu daidai gwagwardon arzikinta”.

Ƙungiyar gwamnoni, wadda ta kunshi dukkan gwamnoni 47 na ƙasar Kenya, ta yi ƙira ga Hukumar SRC da ta dakatar da shirin ƙarin albashin ‘yan siyasa masu riƙe da madafun iko.

Sabon tsarin albashin da aka kawo ya tanadi cewa ɗan majalisar dokoki zai dinga karɓar kuɗin Kenya 739,600 kwatankwancin dalar Amurka 5,730 a kowanne wata, ƙari kan ksh 725,500 kwatankwacin dala 5,620 da suke Karɓa a halin yanzu.

Sabon albashin gwamnoni zai kama ksh 990,000 ($7,620), daga 957,000 ($7,420) da suke karba a yanzu. Ministoci kuma da suke da matsayi iri ɗaya da na gwamnonin za su samu ƙari kwatankwacin na gwamnonin. Kenya na da ministoci 22.

Ƙarin albashin zai janyo kenya ta kashe kusan Sulallan ƙasar biliyan 11 (dala miliyan $85.3) a kowacce shekara, kamar yadda jaridar ƙasa ta Kenya ta rawaito a ranar Laraba.

Matakin janye ƙarin albashin ‘yan siyasar ya zo ne a lokacin da ‘yan ƙasar ke ƙira ga gwamnatin Ruto da ta kawo ƙarshen almubazzaranci a cikin gwamnati.

Zanga-angar adawa da ƙarin haraji da aka yi a baya-bayan nan a Kenya ta janyo asarar rayukan mutum 39, kamar yadda Hukumar Kare Hakkokin Ɗan’adam ta Kenya mallakin gwamnati ta sanar.

Zanga-zangar ta sanya Ruto janye Dokar Kuɗaɗe ta 2024, wadda ta tanadi ƙara yawan haraji a ƙasar.

Leave a Reply