No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kenya ta amince da baiwa ‘yan Afrika izinin shiga ƙasar kyauta

Daga yanzu Kenya za ta ƙyale kusan dukkanin ‘yan Afrika su ziyarci ƙasarta ba tare da neman iznin yin hakan ba, a matsayin sabon umarni daga majalisar zartarwar ƙasar.

Sanarwar da majalisar zartarwar ta fitar ta fayyace cewar za’a soke bukatar neman iznin tafiye-tafiye ga ilahirin ‘yan Afrika, in banda ‘yan kasashen Somaliya da Libya, saboda dalilai na tsaro.

KU KUMA KARANTA:Kenya ta janye shirin ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati

A karkashin tsarin da aka yiwa kwaskwarima, za’a kyale galibin ‘yan Afrika su shiga Kenya kyauta ba tare da neman izini ba tsawon watanni 2.

Buga da kari, za’a kyale mambobin kungiyar kasashen gabashin Afrika-da suka hada da Uganda, Tanzaniya, Rwanda da Burundi-su zauna a kasar tsawon watanni 6 a bisa dacewa da manufar kungiyar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...