Katsina za ta ɗauki sabbin malamai dubu bakwai

2
437

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Katsina ta ce tana shirin ɗaukar malamai na dindindin 7,000 a faɗin ƙananan hukumomin jihar 34.

Babban sakataren yaɗa labarai na Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Katsina.

Malam Ibrahim Kaula ya bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar Malam Faruk Lawal-Jobe ne ya bayyana hakan a wajen ƙaddamar da kwamitin da ke da alhakin gudanar da jarabawar ɗaukar ma’aikata.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta kashe biliyan 57 wajen horar da malamai – UBEC

Lawal-Jobe ya ce gwamnatin jihar ta shirya gudanar da jarabawar ɗaukar ma’aikata ga malaman S-POWER da nufin mayar da su malamai na dindindin.

A cewarsa, kimanin masu masu karatun NCE da Difloma 5,000 da kuma waɗanda suka kammala karatu a ƙarƙashin S-POWER 2,000 a halin yanzu suna koyarwa a makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar.

Lawal-Jobe ya ce shirin na daga cikin ƙudurin gwamnati na inganta harkar ilimi.

“Haka kuma ana son ganin an baiwa ƙwararrun malamai da suka ƙware wajen tsara makomar ɗaliban Katsina,” inji shi.

Ya jaddada muhimmancin yin bitar tsarin ɗaukar ma’aikata na baya-bayan nan wanda ya taimaka wajen ɗaukar ma’aikata 3,889 a hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta jiha (SUBEB).

“Haka kuma za a buƙaci waɗannan mutane da su yi jarabawar ɗaukar ma’aikata iri ɗaya domin tabbatar cancantar su ne kawai suka shiga aikin koyarwa,” inji shi.

Mataimakin gwamnan ya ce tsantsar hanyar da za a yi amfani da ita a duk lokacin ɗaukar ma’aikata ita ce tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Tun da farko, Sakataren gwamnatin jihar, Malam Ahmad Ɗangiwa, ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da ayyukansa ba tare da nuna son kai ba.

Kwamitin wanda Dakta Sabi’u Ɗahiru ya jagoranta, tare da Alhaji Lurwanu Haruna-Gona a matsayin Sakatare, an ba kwamitin wa’adin makonni huɗu ya kammala tare da gabatar da rahotonsa.

2 COMMENTS

Leave a Reply