Katsewar wutar lantarki a Najeriya, ta jefa al’ummar ƙasar cikin duhu

0
34
Katsewar wutar lantarki a Najeriya, ta jefa al'ummar ƙasar cikin duhu

Katsewar wutar lantarki a Najeriya, ta jefa al’ummar ƙasar cikin duhu

Rahotanni sun bayyana cewa an sami tangarɗa ta tsayawar tsarin samar da wutar lantarki na Najeriya ƙasar, sakamakon lalacewar babbar tashar samar da lantarkin.

Wata sanarwar da aka rabawa manema labarai ta adreshin yanar gizo, mai ɗauke da sa hannun kakakin kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu Emeka Ezeh, ta ce lamarin ya auku ne da misalin karfe shida da minti arba’in da biyar na yammacin ranar Litinin.

Ezeh ya ce “lamarin ya shafi duk tashoshin TCN a faɗin ƙasar, saboda haka babu wadatar wuta da za’a baiwa abokan hulɗa.”

Ya ƙara da cewa “wannan lalacewar ta tsarin wutar lantarkin shi ne karo na shida a wannan shekara, kuma tsayawar aikin tsarin ya haifar da duhu a yawancin yankunan ƙasar baki ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Yan ta’adda sun lalata wutar lantarkin Maiduguri zuwa Damaturu

Alkaluman da Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya, NAN ya fitar, sun nuna cewa ma’aunin wutar lantarki na kasar ya durkushe kusan sau 227 a cikin shekaru 14 da suka gabata.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka ƙara kuɗin wutar lantarki a watan Afrilu da kashi 240 cikin 100, wanda ya ƙara dagula wahalhalun da ‘ yan Najeriya ke fuskanta.

Leave a Reply