Kashi 30 na malaman makarantun firamare sun bar aiki a shekaru uku baya — UBEC

0
92
Kashi 30 na malaman makarantun firamare sun bar aiki a shekaru uku baya — UBEC

Kashi 30 na malaman makarantun firamare sun bar aiki a shekaru uku baya — UBEC

Shugaban Hukumar Ilimin Bai-ɗaya na ƙasa, Hamid Bobboyi, ya bayyana cewa sama da kashi 30 na malaman makarantun firamare a Najeriya sun bar aikin a cikin shekaru uku da su ka gabata.

Bobboyi ya bayyana haka ne a yayin wani taron horaswa na kwanaki shida da hukumar kula da ilimin bai-ɗaya ta jihar Kano tare da haɗin gwiwar UBEC suka shirya wa jami’an a jiya Alhamis.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano zai kashe naira biliyan 8 don gina manyan makarantun firamare

Bobboyi, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin tsoro, ya ce wasu malaman sun yi ritaya yayin da wasu kuma suka ajiye aikin don neman wanda ya fishi amma kuma ba a maye guraben su da wasu ba.

Sai dai ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa matakan da ta ke ɗauka na ɗaukar ƙarin malamai da kuma maye gurbin waɗanda suka yi ritaya tare da yin ƙira ga sauran jihohi da su yi koyi da gwamnatin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here