Kashe-kashe da Isra’ila ke aikatawa a Gaza na iya zama ‘laifin yaƙi’ – MƊD 

0
141

An samu rahotanni masu ban tsoro da ke zargin rundunar tsaron Isra’ila IDF da kashe Falasɗinawa aƙalla 11 a yankin Al Remal da ke makwabtaka da Birnin Gaza, a cewar wani rahoto da ofishin hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Falasɗinu da aka mamaye OHCHR OPT ya fitar.

Lamarin wanda ya auku a gaban ‘yan uwan mutanen da aka kashe, ”ya haifar da damuwa tare da sanya firgici game da yiwuwar aikata ”laifin yaki”

Waɗannan zarge-zargen sun biyo bayan ikirarin da ke nuni da cewa sojojin Isra’ila na kai hari tare da kashe fararen-hula, a cewar sanarwar.

La’akari da waɗannan munanan zarge-zarge, hukumar OHCHR OPT ta bukaci hukumomin Isra’ila da su gaggauta kaddamar da wani sahihin bincike mai zaman kansa, kuma Idan har zarge-zargen suka tabbata, ya zama wajibi a hukunta waɗanda ke da hannu wajen aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta bai wa kashi 20 na Falasɗinawan da ke Khan Younis wa’adi

Kazalika hukumar ta ce, dole a ɗauki matakai da za su hana sake faruwar irin waɗannan munanan laifuka sannan akwai buƙatar sa ido sosai a lokutan rikici.

OHCHR ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, tsakanin karfe tara zuwa 11 na dare, lokacin da sojojin Isra’ila suka yi wa ginin Al Awda da aka fi sani da ginin Annan a yankin Al Remal da ke makwabtaka da birnin kawanya tare da kai farmaki cikinsa.

A cewar rahoton, ginin ya kasance matsuguni ga iyalai uku.

A bayanan da shaidu da majiyoyin yada labarai da kuma kungiyar kare hakkin bil’adama ta ”Euro-Med Human Rights” suka rawaito, sun ce an ga yadda sojojin Isra’ila suka mamaye ginin inda suka raba maza da mata da yara sannan suka yi ta harbi har suka kashe akalla mutum 11.

Akasarin mutanen da aka kashe a gaban ‘yan’uwansu ‘yan shekaru sama da 20 ne zuwa 30.

Leave a Reply