No menu items!

Sample Page Title

Date:

KAROTA ta kama direban motar da ya taka fulawar da ake ƙawata titunan birnin Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar kula da zurga zurgar ababen hawa da kiyaye dokokin hanya KAROTA ta kama direban wata motar gida saboda zarginsa da karya dokar tuki.

Hukumar ta karota ta kama direban ne akan titin Murtala Muhammad dake birnin Kano bayan ya tsallaka titi ta wajen da bai dace ba ,tare da taka fulawar titi da gwamnatin Kano ta kawata titin da su.

A wata ganawarsa da manema labarai maimagana da yawun hukumar ta KAROTA Malam Abubakar Ibrahim Sharada yace direban ya karya dokar hanya kuma za’a gabatar dashi a gaban kotu domin zama izinina ga masu kokarin karya dokar tuki a kan hanya.

KU KUMA KARANTA: Hukumar KAROTA a Kano ta gargaɗi masu kai wa jami’anta farmaki

Yaja kunne direbobi da su guji karya dokar hanya,yana mai cewa hukumar ta KAROTA ba zata zura idanu ba.
An Kuma zargin Direban da yiwa yan karota din gadara.
Tunda farko mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada Labarai Hon Ibrahim Adam shine ya wallafa yadda diraban ya karya dokar tuki,kuma hakan yaja hankalin hukumomin da abin ya shafa aka kamo diraban

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...