KAROTA a Kano ta fara gurfanar da masu karya dokokin hanya a gaban kotun tafi da gidanka
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar kula zirga-zirga ababen hawa ta Kano KAROTA ta fara gurfanar da masu karya dokokin hanya a kotun tafi-da-gidanka
Wannan na cikin sanarwar da Mu’azzam Mansur Kurawa, mai taimaka wa shugaban KAROTA kan harkokin yada labarai, ya fitar.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya umarci KAROTA, FRSC da su tilasta wa masu ababen hawa bin dokokin hanya
Sanarwar ta bayyana cewa Shugaban Hukumar, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya jagoranci wannan shirin da ke bai wa hukumar damar gurfanar da masu karya dokokin hanya nan take, domin tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumar KAROTA na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsari da daidaito a harkokin zirga-zirgar ababen hawa a cikin birnin Kano.
Wannan dai na cikin matakan da KAROTA ke ɗauka na cika umarnin da Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya basu, na yin aiki ba sani ba sabo.









