An zargi wasu karnukan Alsatiya guda biyu sun kaiwa wata uwa mai shayarwa mai suna Mummy Basira hari tare da kashe ‘yarta a Unguwar Halleluyah dake Ido-Osun a jihar Osun.
Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe uku na ranar Laraba, 30 ga Agusta, 2023.
Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta ce Mummy Basira na tafiya kan titi da jaririnta a maƙale a bayanta lokacin da ake zargin karnukan sun fito daga ginin mai gidansu ne suka far mata.
Karnukan sun far wa uwar mai shayarwa ne a lokacin da take ƙoƙarin ceto jaririnta mai watanni biyar.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya kashe mutum ɗaya a Bauchi
Mazauna yankin da suka zuba ido ba tare da wani taimako ba a lokacin da karnukan suka kai hari sun bayyana cewa bayan kashe jaririyar, karnukan sun far wa mahaifiyar, inda suka yi mata mummunar illa.
“Dukkanmu mun yi kallo ba tare da komai ba.
An shaida mana cewa karnukan sun yi tsalle daga wani gini da ba kowa a halin yanzu, suka kama jaririyar, inda aka ce ya kai kimanin watanni biyar ɗaure a baya, suka yi mata kaca-kaca.
“Yayin da karnukan suka kama jaririyar, mahaifiyar ta yi ƙoƙarin ceto ta amma ta ka sa. Bayan kashe jaririn, karnukan sun far wa mahaifiyar, inda suka yi mata raunika da dama.
Daga baya wasu mazauna garin sun yi amfani da sanduna wajen fatattakar karnukan tare da ceto mahaifiyar.
An garzaya da ita wani asibiti a nan Osogbo.
“Gidan da karnukan suka fito ba kowa ba ne, amma mazauna wurin sun san waɗanda suke ziyartar wurin.
Suna ta ƙiran lambobin wayarsu, amma an kashe layinsu. A halin yanzu dai tashin hankali ya yi yawa a unguwar. Mun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sandan Estate da ke Osogbo,” in ji ganau Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya bayyana cewa ana ƙoƙarin cafke masu karnukan.
Ta ce rundunar ‘yan sanda za ta ga an yi adalci a cikin wannan hali.