Kare ya farfaɗo da ubangidansa daga dogon suma

0
255

Wani Kare ya yi sanadiyyar farfaɗo da ubangidansa daga wani dogon suma da ya yi inda ake hasashen ba don karen ba, da mutumin ya wuce Lahira.

Lamarin ya faru ne a ɗaya daga cikin ƙasashen Turai ga wani mutum mai suna Francis Romero ɗan shekara 70, inda rahotanni suka ce dattijon ya kwanta rashin lafiya a asibiti inda ya yi dogon suman da bai san wanda ke kansa ba.

A yayin da yake cikin wannan hali ne karensa ya yi zaman dirshan a asibiti a ɗakin da aka kwantar da ubangidan, ya kuma hau gadon da yake kwance ya rungume shi cikin wani hali na ban tausayi.

Hakan ya sa ma’aikata suka ƙyale shi ganin irin shaƙuwar marar lafiya Francis da karen haka suka kwanta har tsawon wata guda a asibitin yana masa jinya.

KU KUMA KARANTA: Ban mamaki: Ɓarayi sunyi satar makudan kuɗi a gidan Gwamnatin Jihar Katsina

Ana cikin haka sai Francis ya farfaɗo daga dogon suman ya tambayi wanda ke kula da shi, inda ya kwatanta shi tamkar mala’ikan rahama da har ta kai a kullum yake yi masa raɗa a kunne cewa ka da ya damu, ya samu ƙarfin jiki zai kuma tashi in Allah Ya yarda.

Ma’aikatan asibitin sun ce masa babu kowa a kusa da shi a kan gadon a kwance sai karenka wanda ya nuna karen ne ya yi masa hakan.

Leave a Reply