Kar ku riƙa biyan kuɗin gyaran transfoma — Kamfanin JED

0
181

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ya shawarci abokan hulɗarsa a Jihar Gombe da kada su biya kowa kuɗin gyara na’urar taransfoma a yankunansu.

Babban jami’in tsaro na JED, Musa Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin cewa, ba hakkin kwastomomi ba ne su gyara taransfoma idan ta lalace.

Abdullahi ya ce ana sa ran jama’a su kai rahoto ofishin JED mafi kusa a duk lokacin da na’urar taransifoma ta samu matsala, kuma kada su biya wani jami’inta kuɗin gyara.

Ya ce ba daidai ba ne a nemi al’umma su ba da gudummawar kudi don gyara ko canza taransfomarsu da ta lalace, hasali ma yaudara ce da kamfanin ba zai lamunta ba.

Jami’in ya shawarci al’ummar jiha da su kai rahoton duk wani ma’aikacinsu da ya nuna irin wannan buƙata domin ɗaukar matakin da ya dace.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta maida wa Nijar wutar lantarki

Ya ce “Ba ma karɓar kuɗi daga hannun al’umma don gyara tiransifoma don haka babu wanda ake tsammanin zai biya.

“Duk ma’aikacin da ya je wurin al’umma karbar kudi a gida-gida ko a kan titi, yaudara ce kuma mun haramta hakan.

“Idan kuna ganin ba za ku iya jira a gyara taransfoma ba, sai ku rubuta wa Manajan Darakta ta hannun Manajan Yankinku cewa kuna son tallafa wa kamfanin don radin kanku ba tilasta muku aka yi ba.

Abdullahi ya kuma yi ƙira ga al’ummar Gombe da su mara wa kokarin kamfanin na kare wutar lantarki a jihar.

Sannan ya yi ƙira da kada a rika cin zarafin jami’an JED da ke bakin aiki, yin hakan laifi ne.

Leave a Reply