Kar a wuce ƙarfe 11 na dare a wuraren taron buki a Kano – Hukumar Hisbah
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar Hisbah ta jaddada cewa har yanzu akwai dokar hana taron biki musamman tsakanin maza da mata, da zarar karfe 11 na dare tayi a jihar Kano.
Mataimakin babban kwamandan Hukumr Hisbah Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan,ta cikin sakon murya da ya turawa da Jaridar Neptune Prime
KU KUMA KARANTA:Matashiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Hisbah
Haka kuma Hukumar ta Hisbah ta haramta zancen dare a Mota a Kano
Malam Mujahideen Ya ce bata gari suna yin amfani da lokutan bukukuwa wajen lalata yan mata.