Kanfanin man NNPC ya rage farashin litar man fetur a Kano da Jigawa

0
48
Kanfanin man NNPC ya rage farashin litar man fetur a Kano da Jigawa

 

Kanfanin man NNPC ya rage farashin litar man fetur a Kano da Jigawa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya umarci gidajen man fetur na shiyar Kano da Jigawa su sauke farashin litar man fetur nan take.

Kamfananin na NNPC yace daga yanzu za’a fara sayar da man fetur akan naira 880 a Kano yayinda a Jigawa kuma za’a koma sayarwa akan naira 920 .

Kamfanin na NNPCL yace za’a cigaba da samun ragin litar man a lokacin zuwa lokaci.

Kafin ragin kamfanin na NNPC na sayar da lita daya akan naira 965 a Jigawa kuma kusan 970.

KU KUMA KARANTA:Yadda NNPC ta yi fatali da tayin Ɗangote na dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya – Obasanjo

A wani sakon murya da Eng Nuraddeen Aliyu wanda daya ne daga cikin manyan dilolin dakon man fetur kuma mai kula da gidan man fetur na NNPC dake tashar mota ta Kano Line , ya aikewa manema labarai yace an tura musu sakon cewa su sauke farashin litar mai a Jigawa da Kano kuma zasu fara aiki da umarnin daga gobe Laraba 5 ga watan Maris zuwa ranar Alhamis 6 ga watan na maris na shekarar 2025.

Yace zasu fara aiki da umarnin ne saboda ragin Yana da yawa kuma, inda yace an daga musu kafa su sayar da man da suke dashi a kasa.

Eng.Nuraddeen Aliyu ya kara dacewa ragin da aka samu yana da nasaba da faruwar danyen man fetur a kasuwannin duniya.

A rana ranar 26 ga watan Fabareru na shekarar 2025 matatar man fetur ta Dangote ta sauke farashin litar man fetur daga naira 890 zuwa 825 albarkacin watan azumin Ramadan kamar yadda matatar Dangoten ta sanar .

Leave a Reply