Kamfanonin sadarwar na ƙoƙarin dawo da ayyukansu, bayan katsewar intanet – NCC

0
175

Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya ta ce kamfanonin sadarwa na ƙoƙarin dawo da sadarwar intanet bayan da ta katse a jiya Alhamis.

Katsewar wayoyin sadarwa a ƙarƙashin teku ya jefa kamfanonin sadarwar nahiyar Afrika cikin gararin katsewar ayyukansu

Masu amfani da na’urorin sadarwa da bankuna sun tsinci kansu cikin garari tsawon sa’o’i sakamakon katsewar intanet wacce ta kassara harkokin sadarwa da hada-hadar kuɗi.

KU KUMA KARANTA:Hukumar NCC ta amince da a sayar da wayoyi 2,155 a Najeriya

Sai dai da sanyin safiyar ranar juma’ar nan, hukumar NCC ta ce ana ƙoƙarin magance matsalar.

Sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na hukumar NCC, Reuben Muoka ya fitar ta bayyana cewar “tuni hukumomin da ke kula da wayoyin sadarwar ƙarƙashin teku sun fara aikin gyaransu, kuma a hankali ayyukansu na dawowa”.

“Hukumomin sun sha alwashin yin aiki ba dare ba rana domin dawo da sadarwar intanet a ƙasashen da al’amarin ya shafa nan da ɗan ƙanƙanin lokaci. Abu ne mai mahimmanci mu sanar da kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen dake hulɗa damu game da halin da ake ciki”.

Haka zalika, hukumar NCC ta bayyana cewar katsewar wayoyin da suka yi sanadiyar lalacewar na’urorin da ke ƙarƙashin teku, sun yi mummunan tasiri akan ayyukan sadarwar intanet dana wayar tarho a ƙasashen yammacin nahiyar Afirka ciki har da Najeriya da Ghana da Senegal da Cote’d Ivore.

Leave a Reply