Kamfanonin sadarwa sun buƙaci ƙara kuɗin ƙira da na data

0
162

Manyan kamfanonin sadarwar da ke aiki a Najeriya (Glo, MTN, Airtel da 9Mobile), sun roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ba su damar ƙara kuɗin kira da na data.

Kamfanonin sadarwar sun buƙaci ga gwamnatin da sakar musu mara ta kuma ba su damar gabatar da batun ƙarin kudin ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

A cewarsu, tsarin ƙayyade musu farashin kuɗin kira da na data na yanzu bai dace da yanayin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati don magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Kamfanonin sadarwan guda huɗu sun ce su kaɗai ne ba su sauya farashinsu ba, wanda kuma hakan barazana ce ga ɗorewarsu da kuma yiyuwar rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ALTON) da Ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar a ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA: Kamfanonin sadarwar na ƙoƙarin dawo da ayyukansu, bayan katsewar intanet – NCC

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, ba a yi wa tsarin farashin gyara na gaba ɗaya ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Sun danganta rashin ƙaruwar farashin ga matsalolin da suka shafi dokar ƙayyade musu farashi, duk da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta

Sun ce: “Tsarin kula da farashi na yanzu, bai dace da yanayin tattalin arziki ba, kuma yana barazana ga ɗorewar kamfanonin kuma yana iya lalata amincin masu zuba jari.

“Duk da taɓarɓarewar tattalin arziki, kamfanonin sadarwa sun kasance masana’anta ɗaya tilo da har yanzu ba ta sake nazarin tsarin farashin ayyukansu ba a cikin shekaru 11 da suka gabata, musamman saboda takunkumin gudanar da tsare-tsare da aka sa musu.

Leave a Reply