Kamfanonin sadarwa na neman gwamnatin tarayya ta ba da damar ƙarin kuɗin katin waya da data na hawa intanet a ƙasar nan.
Majiyoyi daga NCC da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani sun shaida wa Daily Trust cewa, masu amfani da layukan waya a Najeriya za su biya ƙarin 10% zuwa 15% fiye da kuɗin da suke siyan data a yanzu idan buƙatar kamfanonin ta tabbata Legit Hausa ya wallafa.
Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamfanonin sadarwa suka roƙi gwamnati da ta amince da buƙatarsu ta sake yin bitar farashin kuɗaɗen ƙira da data.
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin sadarwa ba su ƙara farashinsu ba tsawon shekaru duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a ƙasar.
KU KUMA KARANTA: Masana kimiyyar sadarwa sun yaba wa NCC kan samar da lambobin bai ɗaya
A halin yanzu, wasu sun lura cewa ƙila kamfanonin sun kasance suna rage ƙarfi da juriyar data don rufe wannan gibi na rashin ƙarin farashi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, ƙungiyar masu lasisin sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta bayyana a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023, cewa tsarin kuɗin ƙira da data a yanzu ba zai kaisu ga madakata ba.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta biya buƙatarsu ba har sai an fara aiki da kasafin kuɗin shekarar 2024 gadan-gadan, kamar yadda wata majiya ta shaida wa The Cable ta ruwaito.
A cewar majiyar, ana ci gaba da nazari da tattaunawa kan yadda ƙarin ba zai shafi talakawan Najeriya ba.