No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kamfanin samar da sukari na Ɗangote ya bayyana cewa ya yi asarar naira biliyan 108.92 a shekarar da ta gabata.

Kamfanin ya danganta asarar da ya tafka da faɗuwar darajar naira, wanda akasari yake sa ribar da kamfanoni suke samu ta zirare.

Kundin bayanan abin da ya faru da shi a 2023, ya bayyana cewa, kamfanin ya yi asarar naira biliyan 172.198 a sakamakon musayar kuɗin Najeriya da na ƙasashen waje.

Asarar ta haddasa raguwar kuɗaɗen masu zuba jari daga naira biliyan 171.2 zuwa naira biliyan 79.2.

Duk da haka raohoton ya nuna cewa a shekarar, kamfanin ya samu karin shigar kudade zuwa  Naira Biliyan 441.453 daga naira biliyan 403.246 da ya samu shekarar 2022.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

Sai dai a zahiri kuma, ribar da aka samu ta ragu zuwa Naira biliyan 86.304 daga Naira Biliyan 91.963 a shekarar 2022, duk da cewa kudin da aka samu ya ƙaru, amma ribar ta zurare.

Dunkulalliyar ribar da kamfanin ya samu kafin ya cire kudin haraji ta ragu zuwa naira biliyan 76.68 idan aka kwatanta da naira biliyan 82.41 da aka samu a shekarar 2022.

Kamfanin ya yi asara bayan cire haraji har ta naira biliyan 73.760 a yayin da ya yi asarar naira biliyan 54.742 a 2022.

Rigar masu zuba jari a kamfanin kuma ya yi kasa da -N6.07 akan kowane hannun jari idan an kwatanta da N4.51 da suka samu a 2022.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...