Kamfanin Emirates ya yi sulhu da gwamnatin Najeriya, zai ci gaba da tashi daga Legas
Kamfanin Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da zirga-zirga tsakanin biranen Legas a Najeriya da Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ranar 1 ga Oktoban 2024.
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da tashi daga Najeriya daga ranar 1 ga Oktoban wannan shekara.
Emirate ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya ce daga nan zai dinga tashi kowace rana tsakanin tsakanin birnin Legas na Najeriya da Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar
Mataimakin kamfanin na Emirates Adnan Kazim ya ce “Muna farin cikin dawo da tashin jiragenmu zuwa Najeriya.”
“Bisa al’ada hanyar Lagos-Dubai ta yi fice a wajen abokan hulɗarmu a Najeriya,” a cewar Adnan.
Ya ƙara da cewa “Muna godewa gwamnatin Nijeriya saboda haɗin kai da taimako wajen sake farfaɗo da wannan hanya, sannan muna fatan yin maraba da fasinjojinmu.”
A watan Agustan 2022 ne, kamfanin na Emirates ya dakatar da safara daga Najeriya, saboda saɓani da gwamnatin ƙasar wajen fitar da kuɗaɗen kamfanin na cinikin da yake yi daga Najeriya.
Gwamnnatin Najeriya ta yi marhabin da matakin na Emirates, inda ta ce dama ta daɗe tana jiran wannan rana.
“Kamfanin Emirates yi babbar sanarwar a hukumance wacce muke jira, Emirates zai ci dawo Nijeriya a wajen Oktoba,” a cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya Festus Keyamo a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.