Kamfanin BUA ya karya farashin buhun siminti zuwa dubu uku da ɗari biyar

0
614

Kamfanin simintin BUA, wanda shi ne kamfanin siminti mafi girma na biyu a kasuwar Najeriya, ya sanar da rage farashin buhun siminti zuwa Naira dubu uku da ɗari biyar (3,500).

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin ya ce sabon farashin zai fara aiki daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Farashin buhun siminti a yanzu haka kafin fitar da sanarwar ya kai kimanin Naira 5,000 kowane buhu ɗaya.

Kamfanin BUA wanda yake mallakin attajirin ɗan kasuwa AbdulSamad Rabiu ne yana da kayan aiki da ke iya samar da siminti tan miliyan 11.

Za mu zuba ido kan yadda dillalai ke siyarwa jama’a kayan BUA ɗin.

KU KUMA KARANTA: Jami’ar Obafemi Awolowo ta rage kuɗin rajistar shiga makarantar

Kamfanin ya kuma sanar da cewar duk waɗanda suka riga suka biya kuɗin kaya a tsohon farashi da ba a kai masu ba za su ci gajiyar wannan ragi da aka yi daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023.

Ya kuma yi ƙira ga dillalai masu lasisi da su tabbatar da ganin cewa masu sayan kaya a hannunsu sun ci gajiyar wannan ragi da kamfanin ya yi inda ya sha alwashin sanya idanu don tabbatar da ganin an bi tsari wajen sayar da simintin.

Leave a Reply